<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>86</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu ya bar Samaniya,
 Yesu ya shigo duniya,
 Yesu ya ji tausayina,
 Mai Cetona!

[V2]
 2) Yesu ya ɗauke laifina,
 Yesu ya sha wahalata,
 Yesu ya mutu domina,
 Mai Cetona!

[V3]
 3) Allah bai ƙyale Ɗansa ba,
 Allah ya ta da baransa,
 Kuma ya kai shi gidansa,
 Mai Cetona!

[V4]
 4) Yesu ya ba ni cetonsa,
 Kada in ƙara zunubi.
 Nan gaba sai in riƙa bin
 Mai Cetona!

[V5]
 5) Yesu, da ni da shi, an ce
 Allah ya haɗa mu sosai,
 Shi ne ya kauda tsorona,
 Mai Cetona!

[V6]
 6) Yesu zai komo duniya,
 Aikinsa duk zai ƙarasa.
 Na sa zuciya ga ganinsa,
 Mai Cetona!</lyrics>
<title>Yesu Ya Bar Samaniya LW86</title>
</song>